Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara inganta harkokin cinikayya da zuba jari na ketare
2020-07-30 09:43:13        cri

Kasar Sin ta bayyana kudirinta na kara daukar matakan inganta harkokin cinikayya da zuba jari na ketare, ta hanyar kara bude kofa da kara gwada ci gaban da aka samu a wasu fannoni na kirkire-kirkiren hidimomi na cinikayya, a wani mataki na kara inganta matakan kasar na bude kofa zuwa mataki na gaba.

An dai cimma wadannan shawarwari ne, yayin taron majalisar gudanarwar kasar na ranar Laraba da firaministan kasar ta Sin Li Keqiang ya jagoranta.

Li ya ce, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci kan daidaita harkokin cinikayya da zuba jari na ketare, inda musamman ya bukaci a bullo da sabbin matakai don ciyar da wannan bangare gaba yadda ya kamata.

Ya ce, abubuwan dake faruwa a waje ne, suka haifar da rashin tabbas din da ake fuskanta a halin yanzu, wadanda kuma suka shafi harkokin cinikayya da zuba jari na ketare kai tsaye. Yana mai cewa, a yayin da ake kokarin inganta muhimman sassan nan guda shida, a hannu guda kuma akwai bukatar kare sassa guda shida. Muddin ana son a cimma wannan buri, wajibi ne a shirya tunkarar sabbin kalubaloli da ka iya kunno kai, musamman wajen daidaita tsarin samarwa da raba kayayyaki na duniya gami da fannonin cinikayya da zuba jari na ketare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China