Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban daban sun bada tabbaci kan yarjejeniyar nukiliyar Iran duk da wasu kalubaloli
2020-09-02 11:03:54        cri
A ranar Talata bangarori daban daban suka bayyana aniyarsu na kiyayewa tare da aiwatar da hadaddiyar yarjejeniyar JCPOA, wacce aka fi sani da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Babban sakataren ayyukan shiga tsakani na kasashen Turai EEAS, Helga Schmid, wanda ya jagoranci taron hadin gwiwar JCPOA, ya wallafa a shafin twitta cewa, mahalarta taron sun amince zasu kiyaye yarjejeniyar ta Iran, kana zasu lalibo hanyar tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar duk da kalubalolin da ake fuskanta.

A sanarwar da aka wallafa a shafin intanet na hukumar EEAS tace, dukkan mahalartan, da suka hada da wakilan kasashen Sin, Faransa, Jamus, Rasha, Birtaniya da Iran, sun jaddada muhimmancin kiyaye yarjejeniyar, sun amince cewa yarjejeniyar wata muhimmiyar hanya ce ta tabbatar da kare duniya daga fuskantar yaduwar makaman nukiliya, kamar yadda kudirin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2231 ya amince.

Fu Cong, babban daraktan sashen hana yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, yace kasar Sin tana fatan dukkannin bangarorin zasu kawar da dukkan banbance banbancen dake tsakaninsu game da batun aiwatar da yarjejeniyar ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna karkasin tsarin yarjejeniyar JCPOA ta hadin gwiwa, kuma su yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu karkashin yarjejeniyar.

Kasancewa yarjejeniyar JCPOA ba zata iya warware dukkan batutuwan tsaro na shiyyar ba, amma zata taka muhimmiyar ruwa karkashin ikon hukumar ta JCPOA, kasar Sin tana goyon bayan sake kafa wani dandalin tattaunawa bayan JCPOA, domin cimma sabuwar matsayar tabbatar da zaman lafiya da tsaron shiyyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China