Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin Da Ake Yi Da Kasar Sin Zai Taimakawa Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya
2020-08-15 20:09:09        cri

"Yanzu, cinikin da ake yi tsakanin kasar Sin da kasar Jamus na samun farfadowa cikin sauri, inda a kan samu jiragen kasa kimanin 45 zuwa 60 dake kaiwa da kawowa tsakanin Duisburg na Jamus da kasar ta Sin a duk mako. Wannan wata jimilla ce da ta fi yawa a tarihi!" A kwanan baya, jaridar El Pais ta kasar Sifaniya ta tsamo wannan maganar da Martin Murrack, darekta mai kula da al'amurran kudi na garin Duisburg na kasar Jamus ya fada. Hakika dai, duk da cewa cutar COVID-19 na ci gaba da bazuwa a kasashe daban daban, amma ana samun karin jiragen kasa masu jigilar kayayyaki tsakanin kasashen Turai da kasar Sin, kana yawan kayayyakin da ake musayar tsakanin bangarorin 2 shi ma ya karu sosai. Wannan wata alama ce da ta nuna yadda cinikin da kasar Sin take yi tare da kasashen waje ke taimakawa farfado da masana'antu da tattalin arziki a kasashe daban daban.

Tun daga farkon shekarar bana, cinikin kasa da kasa ya ragu sosai sakamakon tsanantar yanayin cutar COVID-19 a duniya. Sai dai a nata bangare, kasar Sin ta samu kiyaye bangaren cinikin nata, inda yanayin cinikin da kasar ta yi tsakaninta da sauran kasashe ya fi yadda aka zata a baya, har ma ya wuce na sauran manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki. Alkaluman da muka samu sun nuna cewa, yawan cinikin da kasar Sin take yi tare da kasashen waje yana ta samun karuwa cikin watanni 4 a jere, sa'an nan a fannin shigo da kayayyaki, adadin ma yana karuwa har wasu watanni 2 a jere a nan kasar Sin. Wannan karuwar ba wani abu ne mai sauki ba, ta la'akari da yanayin koma bayan tattalin arzikin duniya, lamarin da ya nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin ke samun cikakkiyar jajircewa.

Wani abun da ya kamata a lura da shi shi ne, ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya sanar da wasu manufofi 15 a kwanan baya don tabbatar da ingancin ciniki da kasashen waje, gami da janyo jari daga ketare. Manufofin da suka hada da kara samar da rancen kudi ga kamfanoni, da taimakawa ciniki ta fasahar shafin yanar gizo ta Intanet, da dai sauransu. Ta wadannan manufofi, ana sa ran ganin kamfanonin kasar Sin masu kula da aikin ciniki da kasashen waje samun karin goyon baya daga gwamnatin kasar.

A lokacin da ake fama da koma bayan tattalin arziki da bazuwar cuta a duniyarmu, yadda kasar Sin take kokarin habaka cinikayya, shi ne domin moriyar kanta, gami da ta kasashen duniya baki daya. Lamarin da ya nuna yadda kasar take kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, musamman ma a fannin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Matakan da kasar Sin ta dauka don habaka ciniki, da sakamakon da ta samu a wannan fanni, za su taimakawa farfado da masana'antu na kasashe daban daban, gami da bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China