Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bunkasar kudin Sin RMB a kasashen waje ta shaida imanin da kasa da kasa suke nunawa Sin
2020-08-17 16:23:58        cri
Rahoton bunkasar kudin Sin RMB na shekarar 2020, wanda babban bankin kasar Sin ya gabatar a kwanakin baya ya shaida cewa, a shekarar 2019, an kara bunkasa kudin Sin RMB a kasashen waje, tun daga bana, bisa halin raguwar ciniki da hada-hadar kudi da tattalin arziki a duniya a sakamakon cutar COVID-19, an kiyaye yin amfani da kudin Sin RMB wajen samun bunkasuwa a kasashen waje. Babu shakka, bunkasar kudin Sin RMB a kasashen waje ta shaida imanin da kasa da kasa suke nunawa Sin.

Bisa kididdigar da aka yi a cikin rahoton, an shaida cewa, yawan kudin RMB da aka yi amfani da su a shekarar 2019 ya kai Yuan triliyan 19.67, adadin da ya karu da kasha 24.1 cikin dari, ya zama matsayin koli a tarihi.

Bisa kididdigar da aka yi, kudin RMB ya zama matsayi na 5 a cikin kudaden da ake yi amfani da su a duk fadin duniya.

Kana a halin yanzu, manyan bankuna na kasashe daban daban ko hukumomin kudi fiye da 70 na duniya sun shigar da kudin RMB a matsayin kudin da ake ajiye da shi a cikin tsarin musayar kudaden da aka adana. Hakan ya shaida cewa, an kara bunkasa amfani da kudin RMB kamar biya kudi, da zuba jari, da tattara kudi, da kuma adana kudade, kana za a yi kokarin bunkasa amfanin kidaya darajar kudade.

Samun karbuwar kudin RMB shi ne sakamakon da aka samu, domin Sin ta kiyaye sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje a fannin hada-hadar kudi. Masana a wannan fanni sun yi nazari cewa, a halin yanzu an samu babban canji a tsarin tattalin arziki da hada-hadar kudi na duniya, idan an fi yin amfani da kudin dala a matsayin musayar kudi da aka adana a duniya, zai haifar da hadarin hada-hadar kudi, ya kamata a yi amfani da kudade daban daban a duniya.

Yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, ba a canja manufar tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin Sin ba, da raya manufofin kudi, da adana cikakkun kudaden waje, da raya karfin tinkarar hadarori, kuma ana fatan za a kara samun amincewa a kasuwar kasa da kasa.

A karshen rabin shekarar bana, za a ci gaba da farfado da bunkasuwar tattalin arzikin Sin, ana fatan za a samun ci gaban tattalin arziki bisa na bara, wanda hakan zai nuna goyon baya ga kiyaye yawan farashin musayar kudin RMB. Kamar yadda mataimakin shugaban hukumar sa ido kan harkokin hannayen jari na kasar Sin Fang Xinghai ya fada a watan Yuni na bana cewa, idan za a kara bunkasa kudin RMB a kasashen duniya, Sin za ta kara inganta karfinta na tinkarar hadarorin hada-hadar kudi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China