Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Ta Cimma Nasarorin Wadata Jama'arta Da Abinci
2020-08-24 17:38:09        cri

Abinci shi ne ruhin rayuwar dukkan halittu, ba a iya rayuwa tilas sai da abinci. Wannan ne dalilin da ya sa mahukunta kasar Sin ke kara azama wajen tabbatar da wadata al'ummar kasar da abinci. A cikin shekaru 71 da suka gabata tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, kasar ta samu manyan nasarori a fannin wadatar abinci lamarin da ya baiwa duniya mamaki duba da yawan jama'ar kasar wanda a bisa kiyasi ya nuna adadin Sinawa ya zarta biliyan 1.4. Wannan kokari ya taimaka matuka lamarin da ya sa kasar Sin ta bayar da babbar gudunmawar kawar da yunwa a duniya, kamar yadda shugaban hukumar adana hatsi da kayayyakin amfanin gona na kasar Sin Zhang Wufeng ya taba bayyana cewa, tun daga shekarar 1949 har zuwa yanzu, a koda yaushe, Sin tana sanya batun magance yunwa a gaban dukkan ayyukan tafiyar da harkokin kasar.

Amma a kwanakin baya, wasu mutane da wasu kafofin yada labaru na yammacin kasashen duniya sun sake "nuna damuwa" kan batun wato ko kasar Sin za ta iya renon al'ummarta da kanta a inuwar bullar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya? Muna musu godiya kwarai sabo da a kullum suna kula da kasancewar Sinawa a duniyar nan.

A karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kasar ta cimma nasarar samar da isasshen abinci bisa namijin kokarin da take yi. Batun samar wa Sinawa isashen abinci yana daga cikin manyan ajandojin jam'iyyar JKS mai mulki a kullum. A karshen makon da ya gabata, babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya ba da wani muhimmin umarni na a daina barnata abinci, inda ya yi nuni da cewa, kowa ya sani cewa duk wata kwayar abinci da wahalar aiki ne ake samunta.

Ko da yake a wannan shekara tasirin cutar numfashi ta COVID-19 da ta addabi duniya tana kuma kawo illa ga tattalin arzikin kasar Sin, amma kasar Sin za ta iya samar da isashen abinci ga al'ummarta. Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar game da yawan kayayyakin gona, musamman shinkafa da kasar za ta samu a wannan shekarar ta 2020 ta nuna cewa, yawan shinkafar da aka samu a kasar a kashin farko a 2020, ya kai ton miliyan 27.29 inda ya karu da ton miliyan 1.08, wato ya karu da 3.9% idan an kwatanta da makamancin lokacin shekatar 2019. Shi ma Ke Bingsheng, tsohon shugaban jami'ar aikin gona ta kasar Sin ya ce, kasar Sin ta samu manyan nasarori ta fuskar wadata kasar da abinci idan an kwatanta da farkon lokacin aiwatar da manufar yin sauye-sauye a gida da bude kofa ga ketare.

Huang Jikun, direktan cibiyar nazarin manufofin aikin gona ta kasar Sin ta jami'ar Peking, ya bayyana a yayin da yake ganawa da wakilin jaridar "The China Science Daily", cewar tsananin kalubale da kasar Sin take fuskanta yanzu shi ne a cikin shekaru 2 ko uku masu zuwa, ko kasar Sin za ta iya rage yawan alkama da shinkafa da ta adana a dakunan adana hatsi. Yanzu yawan hatsin da kowane Basine ya samu ya kai kilogram 474 maimakon kilogram 400 da ya kamata kowane mutumin kasashen duniya ya samu a duk shekara. Kuma yanzu kasar Sin ta kan shigar da wasu kayayyakin gona miliyoyin ton domin renon dabbobin gida kawai. Sabo da haka, ya kamata wadanda suke nuna damuwar batun su kwantar da hankulansu, su yi wanka su shiga barci, ko su mai da hankulansu kan harkokin cikin gidan kasarsu ke nan. Su Sinawa suna iya renon kansu da abincin da suke samarwa da kansu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China