Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sallami mutane 45 daga asibiti a babban yankin kasar Sin bayan sun warke daga COVID-19
2020-08-28 10:28:12        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta sanar a Jumma'ar nan cewa, an sallami mutane 45 daga asibiti a babban yankin kasar Sin jiya Alhamis, bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar numfashi ta COVID-19.

Hukumar ta bayyana cikin rahoton ta na rana-rana da take fitarwa cewa, har yanzu akwai marasa lafiya 288 dake samun kulawar jami'an lafiya, ciki har da mutane 4 dake cikin matsanancin yanayi. Baki daya dai, marasa lafiya 80,091 ne aka tabbatar sun warke daga cutar, an kuma sallame su daga asibiti a jiya.

Ya zuwa jiya Alhamis, baki daya, mutane 85,013 aka tabbatar sun taba kamuwa da cutar a babban yankin kasar, daga cikin su, cutar ta halaka mutane 4,634.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China