Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sin ya zartas da shirin tsara fasalin babban birnin kasa
2020-08-28 11:08:02        cri

Kwanan baya, kwamitin tsakiyar JKS, da majalisar gudanarwar kasar Sin sun zartas da shirin tsara fasalin babban birnin kasar daga shekarar 2018 zuwa shekarar 2035.

Cikin shiri ya jaddada cewa, ya kamata a kiyaye da kuma raya birnin Beijing a matsayinsa na fadar mulkin kasar kana birni na al'umma, ta yadda za a tabbatar da cewa, ana gudanarwar harkokin siyasa yadda kamata a wannan birnin, da warware matsalar da babban birnin ke fuskanta, domin daidaita dangantakar siyasa da tallafawa al'umma kamar yadda ake fata a wannan birni. Da kuma gina birnin da zai dace da yadda ake gudanar da harkokin siyasa, da raya al'adu, da kara jin dadin zaman al'umma.

Haka kuma, shirin ya bukaci a kara kiyaye tsoffin yankunan birnin, da gyara unguwanni da tituna, domin kyautata yanayin zaman al'umma, da inganta shirin kiwon lafiyar al'umma da kuma kare cibiyoyin yankunan birnin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China