Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kokarin tabbatar da hadin gwiwar kabilu daban daban a jihar Xinjiang
2020-08-28 15:47:56        cri
Wasu mutanen kasashen waje na ta shafa bakin fenti kan gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar Sin, wai tana "kyamar wasu kabilu", da neman "cin zarafinsu". Dangane da batun, darekta mai kula da batun kabilu na jihar, Mahmout Usman, ya bayyana a wajen wani taron manema labaru da ya gudana a jiya Alhamis cewa, gwamnatin jihar na kokarin bin dokokin kasar, da aiwatar da manufar kasar dangane da batun kabilu, inda ake tsayawa kan tabbatar da daidaituwa tsakanin kabilu daban daban, da sanya su yi hadin gwiwa don neman samun wadatar bai daya.

A nashi bangare, Yilijan Anayet, kakakin ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang, ya karyata zancen da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka yada, wai cibiyoyin horaswa da aka kafa a jihar Xinjiang sansanin gwale-gwale ne, inda aka kulle 'yan kabilar Uygur a ciki. Ya ce, an kafa cibiyoyin ne don koyar da ilmin sana'a, don biyan bukatu iri daya da na wasu cibiyoyin daidaita tunanin da aka kafa a kasashen Amurka, da Birtaniya, da Faransa. An kafa su ne don daidaita tsatsauran ra'ayin da wasu mutane ke da shi na kaifin kishin addini, da magance yaduwar ra'ayin ta'addanci.

Jami'in ya kara da cewa, jami'an jihar Xinjiang suna nacewa ga wani tunani na maida moriyar jama'a gaban kome, inda suke ta kokarin aiwatar da wasu ayyuka don kyautata zaman rayuwar jama'a, a fannonin samun aikin yi, da ilimi, da ganin likita, da gidajen zama, da dai sauransu. Haka kuma, ana sa ran ganin kawar da talauci baki daya a kauyukan jihar, zuwa karshen shekarar bana. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China