Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta aike kaso na 3 na tallafin kayan yaki da COVID-19 ga Habasha
2020-08-28 10:48:52        cri
Ofishin jakadancin kasar Sin a Habasha ya sanar a ranar Alhamis cewa, ya mika kaso na uku na kayayyakin kiwon lafiya don yaki da annobar COVID-19 ga kasar ta tsakiyar Afrika.

A sanarwar da aka baiwa manema labarai, ofishin jakadancin kasar Sin a Habasha ya ce, kayayyakin lafiyar na yaki da COVID-19 sun hada da takunkumin rufe fuska na jami'an lafiya kimanin 500,000, da kayayakin kare fuska 65,000, da kuma tufafin kariya na jami'an lafiya kimanin 100,000.

Tallafin kayayyakin lafiyar ya hada da dubban safar hannu da jami'an lafiya ke amfani da su, da gilashin rufe fuska, da takalma.

Sanarwar ta ce, tun lokacin da aka samu rahoton farko na bullar cutar COVID-19 a kasar Habasha a tsakiyar watan Maris, gwamnatin kasar Sin, da 'yan kasuwa Sinawa, suke cigaba da bayar da taimako iri daban daban, da nufin taimakawa kokarin da Habasha ke yi na yaki da annobar.

Ofishin jakadancin na Sin dake Habasha ya sanar cewa, tawagar kwararrun masana kiwon lafiyar kasar Sin sun shafe tsawon kwanaki 15 a Habasha a cikin watan Afrilu, a wani bangare na hadin gwiwar jami'an kiwon lafiyar kasashen biyu don yaki da cutar COVID-19. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China