Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayar gudummawar mutum-mutumin gwajin zafin jiki ga filin jirgin saman Burkina Faso
2020-07-24 11:11:27        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin a Burkina Faso ya mika gudummawar mutum-mutumin gwada zafin jiki domin taimakawa filin jirgin saman kasa da kasa na Ouagadougou, wani jami'i ya tabbatar da hakan jiya Alhamis.

Jakadan kasar Sin Li Jian, ya mika gudummawar a ranar Laraba a matsayin wani bangare na kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu. Matakin wata alama ce dake kara nuna goyon bayan kasashe don yaki da annobar COVID-19.

Mutum-mutumin, sabuwar kira ce ta kasar Sin, yana iya auna zafin jikin mutane shida a lokaci guda.

An samar da na'urar ne da nufin kara daukar matakan tsaron yanayin lafiyar jama'a a filin jirgin saman kasa da kasa na Ouagadougou wanda yake shirin dawowa bakin aikinsa.

Babban daraktan hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar Burkina Faso, Hyacinthe Compaore, ya ce wannan tallafi ne wanda ba za'a iya misalta shi ba.

A ranar Laraba, kasar Burkina Faso ta sanar da aniyarta ta sake bude filin jiragen samanta daga ranar 1 ga watan Agusta.

Tun a ranar 21 ga watan Maris, kasar ta yammacin Afrika ta rufe dukkan iyakokinta sakamakon samun rahoton bullar annobar COVID-19 a ranar 9 ga watan Maris.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China