Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kiyaye muhalli don samar da makomar Bil Adama mai kyau cikin hadin kai
2020-08-15 17:32:59        cri

Ranar 15 ga watan Agusta na shekarar 2005, wato lokacin da Xi Jinping,  shugaban kasar Sin na yanzu yana kan mukamin sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake lardin Zhejiang, inda ya gabatar da ra'ayin samun bunkasuwar tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Har zuwa yanzu, shekaru 15 da suka gabata, Sin tana kokarin kyautata tsarinta na kiyaye muhalli da samun ci gaba mai armashi.

Alal misali, ya zuwa shekarar 2019, yawan bishiyoyin da Sin ta dasa ya kai fadin muraba'in mita biliyan 73.9, bisa kididdigar da NASA ta gabatar ta nuna cewa, fadin bishiyoyin da duniya ke dasa ya karu da 5% daga shekarar 2000 zuwa ta 2017, adadin da ya yi kama da fadin gadun daji na Amazon, daga cikinsu gudunmmawar da kasar Sin ta bayar ta kai kashi 25%, wanda ta kai matsayin koli a duk fadin duniya. Ban da wannan kuma, Sin ta cimma nasara matuka wajen rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli da dakile kwararowar Hamada, wadda ta cimma muradun MDD da wuri na hana lalacewar filayen gonaki kafin shekarar 2030.

Duk da cewa, wannan shekarar da muke ciki shekara ce ta karshe a shirin kawar da kangin talauci ga daukacin al'ummar Sinawa, amma wurare daban-daban suna kaiwa ga cimma matsaya daya wato, a guji samun wadata da bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar lahanta muhalli.

Sin ba ta tsayawa kan ci gaba da take samu a cikin gida ba, ta kan dauki wannan nagartaccen ra'ayi cikin hadin kai da take yi da sauran kasashen duniya. Alal misali, yayin da kamfanin kasar Sin ya taimakawa Kenya wajen shimfida layin dogo dake hada Mombasa da Nairobi, ya yi kokarin kiyaye bishiyoyin mangwaro, da kuma bada tabbaci ga kauracewar dabobbi ta hanyar kafa wata hanya ta musamman ga dabobbi dake ratsa wannan layin dogo. A kasar Sri Lanka kuma, kamfanin Sin ya baiwa kasar taimako wajen mayar da tashar ruwa ta Colombo da ta yi amfani da wutar lantarki maimakon man fetur da ta yi a da. Karo na farko ne kasashen kudancin Asiya ke da irin wannan wurin mai amfani da makamashi mai tsabta a tasoshin ruwa nasu. Kazalika, kamfanin Sin ya bada taimako ga tsibirin Bali na Indonesiya wajen yiwa tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da kwal gyaran fuska, wadda ta samar wa mazauna tsibirin wutar lantarki da yawansa ya kai kashi 40%, matakin da ya kiyaye muhallin dake kewayenta. Dadin dadawa, fasahar shuka laima ta yadu zuwa kasashen Afrika ta tsakiya da Fiji, da Laos, da Lesotho da dai sauran kasashe fiye da 100. Ban da wannan kuma, Sin ta ba da gudunmawarta wajen kyautata muhallin nahiyar Afrika, har ma kimiyya da kuma fasahohin kasar Sin sun taimakawa kasashen tsakiyar Asiya wajen cimma burin sauya hamada zuwa wuri mai bishiyoyi. Baya ga wannan kuma, masanan kasashen yankin gabas ta tsakiya sun zo nan kasar Sin don kara ilmi ta fuskar hana kwararowar Hamada da dasa bishiyoyi. Har zuwa yanzu, karin kasashe suna cin gajiyar dabaru da kuma kimiyya da fasahohi da kasar Sin ta samar musu.

Ana iya ganin cewa, ra'ayin samun bunkasuwar tattalin arziki ba tare da bata muhalli ba wanda shugaba Xi Jinping ya gabatar, ba ma kawai ya baiwa Sinawa jagoranci wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye muhalli tare ba, har ma ya taka rawa wajen samar da makoma mai haske wajen kiyaye muhallin duniya baki daya da ma gaggauta raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China