Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Neman Gurgunta Kwalejin Confucius Ba Wani Mataki ne Na Adalci Ba
2020-08-14 20:48:20        cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Mike Pompeo, ya ba da sanarwa a jiya Alhamis, inda ya bayyana cibiyar kwalejin Confucius mai koyar da harshen Sinanci da al'adun Sin dake kasar Amurka, a matsayin tawagar diplomasiyya, har ma ya yi zargin cewa, wai kwalejin Confucius na yin tasiri ga sauran kasashe a madadin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

Ta wannan magana, za mu iya ganin yadda wasu 'yan siyasar kasar Amurka ke neman ta da rikici tsakanin kasashen Sin da Amurka, da shafa kashin kaji kan wani aiki na hadin gwiwa a fannin al'adu da ake yi a tsakanin Sin da Amurka.

A dai jiya Alhamis, cibiyar kwalejin Confucius dake kasar Amurka ta mayar da martanin cewa: Ofishinsu ba ya cikin wata jami'a, sa'an nan ba su taba tsoma baki cikin abubuwan da ake koyarwa a cikin kwalejojin Confucius, da harkar daukar ma'aikata, gami da batun kudi ba. Hakika dai cibiyar ba ta taba samar da wani tasiri kan yadda kwalejojin Confucius dake jami'o'i daban daban na kasar Amurka suke gudanar da ayyukansu ba, balle ma yin wani tasiri "mai illa" a kan su.

Ko da yake kasar Amurka ta yi suna a fannin samun dimbin al'adu na al'ummu daban daban dake zama a kasar. Duk da haka, hukumomin kasar sun dinga matsawa kwajejin Confucius lamba a 'yan shekarun nan. Misali, ma'aikatar tsaron kasar Amurka, da majalisar gudanarwar kasar sun taba gabatar da wasu manufofi, don yin zagon kasa ga ayyukan da kwalejojin Confucius ke gudanar a kasar Amurka, lamarin da ya tilastawa wasu jami'o'in kasar katse hulda da kwalejin Confucius. Hakan ya nuna cewa, wasu 'yan siyasar kasar Amurka dake rungumar ra'ayi na yakin cacar baki, suna kokarin alakanta cudanyar da ake yi tsakanin Sin da Amurka a fannin al'adu, da wasu jayayya da ake yi a fannin ra'ayin siyasa. Ma iya cewa suna matukar tsoron kasar Sin.

Abin da ya kamata a lura da shi, shi ne wannan matakin da kasar Amurka ta dauka don neman gurgunta kwalejin Confucius, ya zo a wani lokacin da huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matukar wuya. Idan mun dan waiwaya baya, za mu ga yadda aka tsoratar da daliban kasar Sin dake karatu a kasar Amurka, da kama su ba tare da wani dalili ba, da yadda aka hana wasu masana na kasar Sin shiga cikin kasar Amurka, da yadda aka kore 'yan jaridun kasar Sin dake Amurka. Hakika wasu 'yan siyasar kasar Amurka na neman toshe hanyar musayar al'adu tsakanin kasarsu da kasar ta Sin.

Sai dai abun da ake yi a kasar Amurka ba wani sabon lamari ba ne Saboda a shekarun 1950, 'yan siyasan kasar Amurka sun taba rungumar ra'ayi na McCarthy, inda suka nuna matukar kiyayya ga masu goyon bayan ra'ayi na Kwaminisanci, tare da aikata abubuwa da yawa marasa kyan gani. Amma kawo wannan zamanin da muke ciki, samun cudanya da hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, wani abu ne da jama'ar kasashen 2 suke son gani, wanda ya dace da moriyar bangarorin 2. Saboda haka yadda ake neman katse huldar dake tsakanin kasashen 2 a fannin al'adu, ba zai haifar da da mai ido ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China