Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikayyar yanar gizo ta samar da karin guraben aikin yi a kasar Sin
2020-08-20 20:56:52        cri

Qiu Jun mai jigilar kayayyakin da aka yi oda a dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo, tun lokacin da ya fara wannan aiki a watan Maris na bana, ya zuwa yanzu, a ko wace rana, yana samun odar kaya kusan guda 40.

Irin wadannan ayyukan da aka samar bisa bunkasuwar tattalin arzikin yanar gizo, sun inganta rayuwa da zaman takewar al'ummar Sin a lokacin annoba. Ya kuma nuna cewa, cinikayyar yanar gizo tana da karfi matuka, kuma za ta iya samar da karin guraben aikin yi.

Kwanan baya, kafar yada labarai ta masu sayayya da kasuwanci ta kasar Amurka wato CNBC ta fidda rahoton cewa, annobar cutar COVID-19 ta gaggauta bunkasuwar harkokin kasuwanci da sayar da kayayyaki ta yanar gizo, yanzu, akwai karin ayyukan da aka samar a kasar Sin dake shafar yanar gizo.

Raya rattalin arziki na yanar gizo ya kasance muhimmin bangaren kare zaman karko a fannin samar da guraben aikin yi a kasar Sin. Kididdigar na nuna cewa, a shekarar 2019, bunkasuwar tattalin arziki na yanar gizo ta ba da gudummawar kaso 67.7% na karuwar GDP baki daya, lamarin da ya nuna muhimmancin cinikayyar yanar gizo. A shekarar 2019 da shekarar 2020 kuma, kasar Sin ta gabatar da wasu sabbin nau'o'in ayyuka guda 29, kuma 75% daga cikinsu, sun shafi tattalin arziki na yanar gizo.

A hakika, cinikayyar yanar gizo tana raya sabbin sana'o'i a kasar Sin, yadda za a bunkasa wannan aiki zai taimaka matuka wajen raya tattalin arzikin kasar Sin baki daya, baya ga samar da karin guraben aikin yi a kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China