Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNECA ta kaddamar da cibiyar sanya ido kan farashin kayayyaki ta farko a Afirka
2020-08-14 11:09:26        cri

Hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arzikin Afirka (ECA) a jiya Alhamis ta sanar da kaddamar da wata cibiyar kula da bambancin farashin kayayyaki a matakin kasashe, da shiyyar tattalin arziki da nahiyar Afirka baki daya.

A cewar hukumar ta ECA, manufar kafa sabuwar cibiyar wadda ita ce irinta ta farko, sun hada da hade farashi da darajar musayar kudaden ketare a dukkan kasashen Afirka karkashin laima guda, ta yadda al'ummomin nahiyar, da masu tsara manufofi da ragowar masu ruwa da tsaki za su iya samu cikin sauki.

Haka kuma cibiyar za ta rika yin karin haske kan hauhawar farashin kayayyaki a kowa ne wata, da bayan watanni hurhudu da ma bayan shekara. Ta kuma jaddada cewa, kaddamar da cibiyar ta zo a lokacin da gwamnatoci ke son sanin irin tasirin da annobar COVID-19 ta yiwa karfin al'umma na sayan muhimman kayayyakin bukatun rayuwa, yayin da kasashen ke ci gaba da aiwatar da matakan kulle.

Bikin kaddamar da cibiyar da aka gudanar ta kafar bidiyo, ya samu halartar manyan shugabannin Afirka da ministoci kudi da na raya tattalin arziki da wakilan ofisoshin kididdiga daga sassan Afirka, wadanda suka yi na'am da matsayinsu na manyan masu ruwa da tsaki a wannan shiri, inda suka yi alkawarin ba da gudummawa wajen tattara alkaluman da ake bukata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China