Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni masu jarin waje dake da idon basira ba za su bar kasar Sin ba
2020-08-16 16:17:56        cri

Koda yake, 'yan siyasar kasar Amurka suna ci gaba da sa kaimi ga kamfanonin kasar dake kasar Sin da su bar kasar Sin, amma, wani rahoton da kwamitin cinikayya na Sin da Amurka ya gabatar a kwanan baya ya nuna cewa, cikin kamfanoni masu jarin Amurka dake kasar Sin da ya yi bincike, kashi 83% daga cikinsu sun dauki kasuwar kasar Sin a matsayin kasuwa mafi muhimmanci, ko kuma, daya daga cikin manyan kasuwanni 5 nasu. Kuma kashi 75% daga cikin wadannan kamfanoni za su zuba jari a shekara mai zuwa kamar yadda suka yi a baya, ko kuma kara jarin da za su zuba a Sin. Kamar yadda ministan harkokin kasuwancin kasar Sin Zhong Shan ya ce, kamfanoni masu jarin waje dake da idon basira ba za su bar kasar Sin ba.

Akwai jerin rahotannin da aka fidda, wadanda suka nuna karfin tattalin arzikin kasar Sin, da ma bunkasuwar kasuwannin kasar Sin, lamarin da ya janyo hankulan kamfanonin ketare sosai. A watan Yuli, adadin jarin waje da aka yi amfani da su a fadin kasar Sin ya kai kudin Sin yuan biliyan 63.47, wanda ya karu da kashi 15.8% idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara. Lamarin da ya nuna cewa, Sin ta samu karuwar jarin waje cikin watanni 4 da suka gabata.

Cikin watanni 7 da suka gabata kuma, Sin ta yi amfani da jarin waje da adadinsu ya kai yuan biliyan 535.65, wanda ya karu da 0.5%, 'yan kasuwan kasashen ketare sun kafa sabbin kamfanoni guda 18,838 a kasar Sin, kana, an gaggauta aiwatar da wasu manyan shirye-shiryen kamfanoni masu jarin waje. Haka zalika kuma, wasu manyan kamfanonin kasashen ketare da suka hada da, kamfanin man fetur na Exxon Mobil, da kamfanin motoci na BMW, da kuma kamfanin motocin Toyota da sauransu, suna ci gaba da kara zuba jari a kasar Sin.

Idan muka duba yanayin kasuwanci na yanzu, za a gane cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta haddasa babbar asarar harkokin zuba jari tsakanin kasa da kasa, barin kasar Sin bai dace da ka'idar kasuwanci ba, sai kara zuba jari a kasar Sin shi ne dabarar basira. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China