Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gudanar da taro na 6 game da yanar gizo a wata mai zuwa
2019-09-18 20:28:45        cri

Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron kasa da kasa karo na 6 game da yanar gizo a watan Oktoba mai zuwa, a garin Wuzhen dake lardin Zhejiang na gabashin kasar, kamar dai yadda hukumar dake lura da al'amuran da suka jibanci yanar gizo ta kasar, ko CAC a tabbatar da hakan a Larabar nan.

Da yake karin haske game da makasudin taron, yayin taron manema labarai da aka gudanar, mataimakin daraktan hukumar ta CAC Liu Liehong, ya ce taron na yanar gizo zai gudana ne tsakanin ranekun 20 zuwa 22 ga watan Oktoba. An kuma sa masa taken "dabaru, da hade sassa, bude kofa da hadin gwiwa: gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama tare."

Yayin taron za a gudanar da kananan dandali 20, wadanda za su shafi tattauna batutuwa da ake maida hankali a kan su, kamar kwaikwayon tunanin bil Adama, da fasahar 5G, da zamanantar da masana'antu ta hanyar amfani da na'urori.

Za a yi amfani da taron na kasa da kasa, wajen nazartar sabbin dabarun kimiyya da fasaha, da raya masana'antu da tattalin arziki, da inganta rayuwar al'umma, da hadin kai tare da kyautata salon jagoranci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China