Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harkokin tattalin arziki na ci gaba da farfadowa a kasar Sin
2020-08-10 15:32:54        cri

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin na nuna cewa, farashin kayayyakin da masana'antun kasar ke samarwa, ya ci gaba da faduwa a watan Yulin, amma faduwar ta ci gaba da raguwa, yayin da harkokin tattalin arziki ke farfadowa bayan da kasar ta yi nasarar dakile yaduwar cutar COVID-19.

Hukumar ta ce alkaluman farashin na PPI, wanda ke kimaninta farashin kayayyaki a mashigar masana'antu, ya ragu da kaso 2.4 cikin 100 kan na watan Yulin shekarar da ta gabata. Kana a cikin wata guda, baki dayan farashin kayayyakin ya karu da kaso 0.4 cikin 100, yayin da harkokin masana'antun ke ci gaba da kankama, bukatun kasuwa na farfadowa yadda ya kamata, baya ga yadda shi ma farashin kayayyaki na kasa da kasa ya taka muhimmiyar rawa.

Alkaluman na PPI na zuwa ne, yayin da aka fitar da bayanai game da farashin kaya da jama'a ke saya (CPI) wanda ke nuna yadda farashin kayayyakin ya tashi zuwa kaso 2.7 cikin 100 a watan Yuli sama da farashin abinci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China