Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jita-jitar Siyasa Ta Yi Illa Ga Rayukan Amurkawa
2020-08-18 21:39:04        cri

Kwanan baya, shugabannin kasar Amurka sun sha yin amfani da kalmomin "annobar Sin" ko kuma "kwayar cutar Sin" wajen bayyana cutar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya bata ran al'ummomin kasa da kasa. Kafar watsa labarai ta CNN ta kasar Amurka ta ce, kasashen duniya sun riga sun cimma matsayi daya kan yadda za a kira wannan cuta, a maimakon "cutar Sin" da makamantansu.

Shi ma George Packer ya wallafa wani sharhi a mujallar The Atlantic ta kasar Amurka cewa, shugabannin kasar Amurka sun dauki wannan annoba a matsayin harkar siyasa. Wasu mutane sun kuma bayyana cewa, saboda matsin lamba ganin yadda babban zaben kasar ke karatowa, yadda 'yan siyasan kasar Amurka suke yin karya ga al'ummomin kasar, zai sa su zama abin dariya.

Kamar yadda masana kimiyya suka bayyana cewa, yaduwar annoba ta kasance babban kalubale ga dukkanin al'ummomin duniya. Mai iyuwa, 'yan siyasa za su cimma burinsu ta hanyar yin karya ko cin zarafin wata kasa, amma, ba hakan zai taimaka wajen yaki da cutar ba. Kuma, yadda 'yan siyasan kasar Amurka suke neman alakanta cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin, ya kara sabanin dake tsakanin al'ummomi daban daban a cikin kasar Amurka, lamarin da ya haifar da karin barazana ga al'ummomin kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China