Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rigakafin COVID-19 da Sin ke shirin samarwa ba shi da illa ga bil adama
2020-08-17 17:07:37        cri

Masu hikimar magana na cewa rigakafi ya fi magani. Tun bayan barkewar annobar shakewar numfashi ta COVID-19 a farkon wannan shekara, baki daya za'a iya cewa hankulan masanan kiwon lafiya na kasa da kasa ya karkata wajen ayyukan yaki da annobar wacce ke zama a matsayin babbar barazana ga dukkan bil adama, musamman bisa ga yadda annobar ta zama karfen kafa wajen tabarbarewar tattalin arzikin duniya da sauya yanayin zaman rayuwar al'ummar kasa da kasa. Sai dai masana kiwon lafiya na duniya sun yi ittifaki cewa, babban abin da zai iya zama maslaha wajen daidaita batun yanayin lafiyar al'ummar duniya bai takaita kan magungunan warkar da masara lafiyar da suka kamu da cutar ta COVID-19 ba. Masanan dai sun yi amanna cewa, hanya daya tilo da za ta zama mafita ga duniya ita ce, binciken yadda za'a samar da rigakafin cutar, kuma muddin ba'a samu rigakafin cutar ba, to za'a iya cewa tsugune ba ta kare ba. Wasu ma na ganin cewa ko da mutanen da suka kamu da cutar sun warke, to tamkar maganar nan ne da 'yan magana ke cewa an kashe maciji amma ba'a sare kansa ba. Wannan dalili ya sa masanan kasa da kasa suka dukufa wajen neman mafita, wato samar da alluran rigakafin cutar. Kasar Sin tana daga cikin kasashen da suka dukufa wajen aikin binciken samar da rigakafin cutar ta COVID-19, kuma kawo yanzu, aikin binciken samar da rigakafin ya yi nisa matuka. Kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Journal of the American Medical Association ta fitar a wannan mako ta nuna cewa, alkaluman sakamakon gwajin rigakafin annobar COVID-19 wanda kasar Sin ta samar yana cikin yanayi mai inganci, kuma yana samar da kyakkyawan sakamako. Takardar bayanan binciken ta yi tsokaci kan mataki na 1 da na 2 na sakamakon gwajin alluran rigakafin cutar ta COVID-19 wanda cibiyar gwajin kwayoyin halittu ta Wuhan karkashin hukumar kula da kimiyyar halittu ta kasar Sin CNBG, suka gudanar, karkashin kwalejin nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin.

Binciken ya kunshi bayanan da aka samu daga mutane 320 da aka yiwa gwajin rigakafin 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 59, wadanda suka amince bisa radin kansu, inda aka yiwa mutane 96 gwajin a zagaye na 1, da kuma mutane 224 da aka yiwa gwajin a zagaye na 2 na rigakafin.

Sakamakon ya gwada cewa, rigakafin yana da matukar inganci ta fuskar samar da garkuwa ga jikin mutanen da aka yi wa gwajin, sannan, karfin da rigakafin ke da shi yana da matukar tasiri wajen baiwa jiki kariya. Takardar binciken ta nazarci inganci rigakafin, sakamakon ya gwada cewa, rigakafin ba shi da wani illa mai yawa ga jikin dan adam. Abin da kawai ya fi zama damuwa shi ne, zafin da za'a iya ji a sashin jikin da aka yiwa allurar, sai kuma dan zazzabi kadan dake iya biyo bayan allurar, sai dai dukkansu ba matsaloli ne da za su iya yin tasiri na a zo a gani ga jikin dan Adam ba. Bugu da kari, binciken ya tabbatar da cewa rigakafin ba zai taba illata gangar jiki ko lafiyar dan adam. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China