2020-08-12 14:08:51 cri |
A ranar 7 ga wata, wakilin kamfanin dillancin labarai na NBC na kasar Amurka ya kai ziyara cibiyar nazarin kwayoyin cuta ta birnin Wuhan, inda ya zanta da kwararrun cibiyar da dama, ciki har da shugabar cibiyar Wang Yanyi.
A yayin zantawar tasu, Wang Yanyi ta ce, ita da sauran ma'aikatan cibiyar ba su ji dadin abubuwa na rashin adalci da suka faru a gare su ba.
Ta ce, cibiyar nazarin kwayoyin cututtuta ta birnin Wuhan ta yi nasara a fannin nazarin kwayoyin cututtuka da yaki da cutar, ta kuma fitar da allurar rigakafin kwayar cutar SARS-CoV-2 ta farko a duniya. Amma, abin bakin ciki shi ne, wasu sun mai da cibiyar a matsayin asalin kwayar cutar COVID-19.
Haka kuma, ta ce, babu masanin cibiyar ko daya da ya kamu da cutar COVID-19, kuma, bai kamata a hana aikin binciken asalin kwayar cutar ba, sabo da wasu dalilan na siyasa.
A zantawarsa da wakilin kamfanin dillancin albarai na NBC, shugaban sashen birnin Wuhan na cibiyar nazarin ayyukan kimiyya ta kasar Sin, kana, masanin cibiyar nazarin kwayoyin cutar birnin Wuhan, Yuan Zhiming ya musanta zargin da ake game da asalin kwayar cutar COVID-19.
Sama da shekaru 16 kungiyar EcoHealth ta birnin New York tana hadin gwiwa da cibiyar nazarin kwayoyin cuta ta birnin Wuhan. Shugaban kungiyar Peter Daszak ya bayyana cewa, cibiyar nazarin kwayoyin cuta ta birnin Wuhan ba ta boye kome ba, ta gabatar da yanayin yaduwar kwayar cutar numfashi ta COVID-19 cikin sauri, kuma, babu shaidun da suka nuna cewa, cutar ta samo asali ne daga dakin gwajin cibiyar. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China