Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kan Nijeriya da Ghana zai kawo ci gaba a yankin yammacin Afrika
2020-08-18 18:56:47        cri

Kasancewar Nijeriya da Ghana manyan kasashe kuma makotan juna, sannan 'yan uwa masu daddadiyar dangantaka, kana manyan abokan cinikayya, kyautata mu'amalarsu zai karawa yankinsu kwanciyar hankali da ci gaba.

Ko kadan sauyawar kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu bai dace da su da al'ummominsu ba, bisa la'akari da yadda al'ummomin na suke zaman 'yan uwa kuma masu kamanceceniya a fannoni da dama.

Duniya ta ci gaba a fannoni da dama, haka zalika, kan al'ummomin duniya ya waye sosai fiye da baya. Bai kamata a ce a wannan lokaci da kan kowa ya waye sannan aka ilmantu, a ce ana ci gaba da samu matsala irin wadanda aka samu a da can baya shekaru da dama da suka shude ba. Yadda al'amuran duniya ke tafiya, kama daga rashin tabbas zuwa kalubale iri-iri, ya kamata a ce zuwa yanzu an dauki darasi, an gane cewa, makomar dukkan bil adama na hade da juna. Yadda wadannan kalubale da matsaloli da ake fuskanta ba sa la'akari da banbancin jinsi ko launi ko iyakar kasa, kamata ya yi al'ummomin kasa da kasa su fahimta cewa, ba su da abun dogaro da ya wuce junansu.

Idan har kasashen yanki guda dake da tasiri irin Nijeriya da Ghana za su ci gaba da rikici da juna, ina ga kananan kasashe ko kuma kasashen da ba su hada alaka ta komai ba?

A wannan lokaci da ake fuskantar matsalar tattalin arziki da annobar COVID-19 da ayyukan 'yan ta'adda, ake kuma rajin tabbatar da dunkulewar duniya da bunkasa dangantakar kasa da kasa har ma da aiwatar da cinikayya mara shinge, kamata ya yi gwamnatocin kasashen da dukkan masu ruwa da tsaki, su yi kokarin lalubo bakin zaren domin samun maslaha. Yanzu lokaci ne da ake ta kira da a hada kai domin farfado da tattalin arzikin duniya da samar da ci gaba da kuma tunkarar kalubale na bai daya a tare.

A matsayin manyan kasashe a yankin yammacin Afrika, kyakkyawar dangantakar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Ghana na da matukar muhimmanci ga yankin da ma nahiyar Afrika baki daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China