Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da dama a Najeriya
2020-08-13 09:52:02        cri

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya, John Enenche ya bayyana cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama, biyo bayan wasu hare-hare ta sama da suka kaddamar a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kakakin ya ce, sojojin sun kuma yi nasarar lalata makaman da 'yan ta'addan ke amfani da su a yankin Gulumba Gana-Kumshe dake jihar ta Borno a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce, sojojin sun yi nasarar gano wurin da mayakan ke labewa suna kaddamar da hare-hare kan sojoji a wannan yanki. Hare-hare ta sama da sojojin suka kaddamar, na zuwa ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukan 'yan ta'addan da jerin shawagi liken asiri ta sama dake nuna tarin 'yan ta'addan a wannan yanki, da maboyarsu da ma wuraren da suke yin taro.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China