Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun kashe mutane 14 a Najeriya
2020-08-14 12:39:26        cri

Hukumomin 'yan sandan a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 14 yayin wani hari da 'yan bindiga suka kaddamar a jahar Neja dake shiyyar arewa ta tsakiyar kasar.

Wasu mutanen biyar sun samu raunukan harbin bindiga a lokacin harin wanda aka kaddamar a kauyen Ukuru dake karamar hukumar Mariga na jahar, Wasiu Abiodun, kakakin 'yan sandan jahar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Abiodun ya ce, ana zargin maharan barayi ne, kuma wasu daga cikinsu ma barayin shanu ne.

A cewar Ashafa Maikera, shugaban 'yan kato da gora na kauyen, 'yan bindigar sun shiga kauyen ne akan babura sama da guda 50 a cikin dare inda suka kaddamar da harin.

Maikera ya ce, ya zuwa yanzu sun samu gawarwakin maza 13 da gawar mace daya bayan harin. Hudu daga cikin 'yan kato da gora na kauyen suna daga cikin wadanda aka hallaka a harin.

'Yan sanda sun ce, suna ci gaba da gudanar da bincike game da harin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China