Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NEMA ta yi gargadin samun mummunan ambaliyar ruwa a jihar Kano a wannan shekara
2020-08-13 11:15:27        cri

Wani sabon gargadi da hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta fitar a jiya Laraba, na nuna cewa, akwai yiwuwar jihar Kano mafi yawan al'umma dake arewacin kasar, za ta fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a wannan shekara, matsalar da ake hasashe za ta shafi kananan hukumomi 20 na jihar.

A don haka ne ma, Jami'in hukumar ta NEMA a jihar Kano Sanusi Ado, ya yi kira da a hada karfi da karfe, don tabbatar da cewa an shirya tunkarar tasirin da ambaliyar da ake hasashe za ta iya haifarwa a wannan shekara, yayin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19.

Sanusi Ado ya ce, galibi irin wannan ambaliya na barazana ga bangaren aikin gona, da albarkatun ruwa da lafiya da sufuri game da fannonin more rayuwa a jihar.

Shekaru takwas da suka gabata ma, jihar ta Kano ta yi fama da matsalar ambaliyar ruwa, wadda ta raba dubban mutane da muhallansu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China