Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar Daily Trust ta musunta yadda kasar Sin ta yi wa Nijeriya tarko ta hanyar bin bashi
2020-08-12 13:10:20        cri

Kwanan baya, jaridar Daily Trust ta kasar Nijeriya ta wallafa wani sharhin da Gimba Kakanda ya rubuta, inda ya musunta yadda wasu ke cewa, wai kasar Sin ta danawa Nijeriya tarkon bashi.

Sharhin ya ce, a 'yan kwanakin baya, wasu kafofin yada labaru na kasar sun yi shelar cewa, yarjejeniyar da Nijeriya ta kulla na samun rance daga Sin za ta illata 'yancin kasar. Hakika wannan zance ba shi da kan gado, abin dariya ne. Idan har ana maganar batun 'yancin kasa, to, ya kamata mu waiwayi yadda Nijeriya ta karbo rancen kudi daga hukumomin hada-hadar kudi karkashin tsarin Bretton Woods a shekaru 1980 zuwa 1990, ta kuma yi gyare-gyare kan tsare-tsarenta yayin da asusun ba da lamuni na duniya da bankin duniya suka tsoma baki a ciki, lamarin da ya raunata mulkin kan kasa ta fuskar tattalin arziki.

Sin da Nijeriya, aminai ne da ke hadin gwiwa a tsakaninsu domin samun moriyar juna. Nijeriya kasa ce dake kan gaba a fannin sayen kaya daga kasar Sin, kana ita ce kasa ta biyu a Afirka da kasar Sin ta fi zuba jari. Yanzu haka bunkasa da habaka hadin gwiwa a tsakaninta da Sin ya dace da muradun Nijeriya.

Samun rancen kudi daga kasashen ketare kan haddasa barazana da dammamaki, amma dole ne a mai da hankali kan yadda za a yi amfani da kudaden da aka ranto. Wata rana man fetur, iskar gas za su kare. Abun da ya dace kana dole Nijeriya da sauran kasashen duniya su yi shi ne yin amfani da albarkatun da Allah ya hore musu yadda ya kamata, tun kafin su kare, su kyautata tsarin tattalin arzikinsu, su kara karfinsu ta fuskar tattalin arziki, a kokarin kama hanyar raya kasa mai dorewa cikin hanzari. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China