Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar Africa CDC ta yi kira da a rika kiyaye matakan kandagarki
2020-08-08 16:56:55        cri

Yayin da adadin masu COVID-19 ke ci gaba da karuwa a nahiyar Afrika, cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Africa CDC, ta bukaci a kara kiyaye matakan tabbatar da lafiyar al'umma a fadin nahiyar.

A cewar cibiyar, adadin masu cutar a fadin nahiyar, ya haura miliyan guda, inda ya kai 1,007,366 zuwa yammacin jiya Juma'a.

A jawabinsa na kaddamar da makon makarin hanci da baki ta duniya, da aka ware daga ranar 7 zuwa 14 ga watan Agusta da nufin kara yawan amfani da shi a wuraren dake da taron jama'a, Daraktan cibiyar, John Nkengasong, ya ce dole ne a kara yawaita sanya makarin baki da hanci yayin da ake fadada ayyukan gwaji da na jinya.

Ya ce duba da yadda adadin masu kamuwa da cutar ke karuwa a nahiyar da ma duniya baki daya, ci gaba da sanya makarin na da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwar cutar, duk da cewa yanayin ya banbanta a sassan duniya.

Ya kara da cewa, kafin a samu riga kafi da magungunan yaki da cutar, rufe fuska shi ne ingantacciyar dabarar da ake da ita, musammam a inda ba a nisantar juna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China