Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kiyaye muhalli tare da wadatar da mutane
2020-08-14 15:11:34        cri
Kafofin yada labaru na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin sun ruwaito cewa, daga shekarar 2016 ya zuwa yanzu, an mayar da shirye-shiryen yawon shakatawa guda 8 a matsayin wata hanyar taimakawa wajen yaki da talauci a kasar Sin. Kana kuma an tanadi kauyuka guda 8 a lardin cikin jerin sunayen manyan kauyukan kasar Sin ta fuskar yin tafiye-tafiye. Iyalai fiye da dubu 15 masu mutane kusan dubu 58 sun fita daga kangin talauci ta hanyar gudanar da ayyukan yawon shakatawa.

A bana ne mahukuntan kasar Sin, suka tsara kammala babban aikin raya al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, da ta kawo karshen aikin fitar da al'ummar kasar baki daya daga kangin talauci. Neman cin gajiyar wurare masu ni'ima, wata kyakkyar hanya ce ta samun nasarar fitar da dukkan al'ummar Sin daga kangin talauci. Ga wasu wurare masu fama da talauci, dukiya mafi daraja gare su ita ce albarkatun muhallin halittu, kuma abun da suka fi sauran wurare kyau shi ne kyawawan albarkatun muhallin halittu. Don haka yin kokarin raya wurare masu ni'ima a wurin, hanya ce mai dacewa wajen fitar da su daga kangin talauci cikin hanzari da kuma raya kansu bisa matsakaicin wadata. Alkaluma na nuna cewa, yawan mutanen da aka fitar daga kangin talauci ta hanyar aikin yawon shakatawa ya kai kaso 17 zuwa 20 cikin 100 na jimillar mutanen da ake kokarin fitar da su daga talauci a nan kasar Sin. Karin mutane wadanda suka taba fama da tsananin talauci sun fara sha'aninsu da ke da nasaba da aikin yawon shakatawa, sun kuma fara jin dadin zaman rayuwarsu a kwanan a tashi. Idan har muka ci gaba da kiyaye muhalli mai kyau, to, hakan zai taimaka mana wajen fitar da mutane daga kangin talauci yadda ya kamata.

Yau shekaru 15 ke nan, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da tunanin "muhalli mai kyau zai haifar da alfanu da bunkasar tattalin arziki", wanda ya ba da jagora kan yadda za a samu daidaito tsakanin raya kasa da kuma kiyaye muhalli a nan kasar Sin. Kana tunanin ya kasance jagora ga kasar Sin game da hanyar bunkasa tattalin arziki tare da kiyaye muhallin halittu, kana ya zama abin koyi ga wasu kasashe maso tasowa. Tabbas ne kasar Sin za ta samu wadata da kuma muhalli mai ni'ima ta wannan hanya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China