Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gabatarwa masanan Nijeriya matakan kasar Sin na yaki da cutar numfashi
2020-02-14 12:17:43        cri

A jiya ne, cibiyar nazarin Sin ta kasar Nijeriya ta shirya wani taro a Abuja, babban birnin kasar, inda aka gayyaci jakadan Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian don gabatarwa masana da 'yan jaridun kasar, matakan da kasar Sin take wajen yaki da cutar numfashi da ta bulla a kasar. Wakilai daga cibiyar nazarin zaman lafiya da daidaita rikice-rikice ta kasar Nijeriya, da cibiyar nazarin tattalin arzikin Afirka, da jami'ar Abuja, da jaridar Leardership da sauransu sun halarci taron.

Jakada Zhou Pingjian ya yi cikakken bayani game da kokarin da Sin ta yi wajen yaki da cutar da ma ci gaban da ta samu. Ya ce, Sin ta dauki managartan matakai don hana yaduwar cutar, da tabbatar da tsaro da kare lafiyar jama'ar kasar Sin, kana ta samar da gudummawa wajen tabbatar da kare lafiyar al'ummar duniya. Sin da Afirka sun ga bayan cutar Ebola, kuma a halin yanzu kasashen Afirka sun nuna goyon baya ga kasar Sin wajen yaki da cutar numfashi da ta bulla a kasar ta hanyoyi daban daban. Sin tana son kiyaye yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kasar Nijeriya wajen kare lafiyar jama'ar kasashen biyu.

Direktan cibiyar nazarin Sin ta kasar Nijeriya ya bayyana cewa, ayyukan yaki da cutar numfashin na kasar Sin sun nuna karfin kasar Sin da yadda kasar take kula da tsaron al'ummar duniya, da matakan da aka dauka bisa tunanin shugaba Xi Jinping na raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, wanda zai haifar da nagartaccen tasiri a nan gaba. Babban edita na jaridar Pilot ta Nijeriya ya bayyana cewa, Sin ta dauki matakan da suka dace na yaki da cutar cikin sauri, wadanda da wuya a ga yadda wata kasa ta dau irin wannan matakan a lokacin da ake samun annoba. Duk da haka wasu kasashe suna neman yin amfani da wannan dama don zargi da ma bata sunan kasar Sin, don haka bai kamata mu yi imani da su ba, in ji babban editan. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China