Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saifullahi Aminu Bello: Jami'armu na kokarin kare mu daga kamuwa da cutar COVID-19
2020-03-05 11:52:11        cri

A yayin da gwamnatin kasar Sin ke ci gaba da yakar annobar cutar numfashi ta COVID-19, wakilin sashin Hausa na CRI Murtala Zhang ya zanta da wasu daliban Najeriya dake karatu a wurare daban-daban na kasar, don jin ta bakinsu kan yadda gwamnatin kasar ke kokarin kare su daga kamuwa da wannan cuta.

Saifullahi Aminu Bello, wani dan jihar Kano ne wanda ke karatun digiri na uku a fannin na'ura mai kwakwalwa dake jami'ar Xiamen a lardin Fujian dake kudancin kasar Sin. A zantawarsa da Murtala Zhang, Saifullahi Bello ya ce, kwalliya tana biyan kudin sabulu wajen yakar wannan cuta, kuma ana sake bude wasu lambunan shan iska da shaguna da kasuwanni dake wurin yayin da harkokin rayuwar mazauna wurin ke farfadowa.

Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.


 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China