Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 118 sun rasu sakamakon musayar wuta tsakanin sojojin gwamnati da masu dauke da makamai a Sudan ta Kudu
2020-08-12 12:05:31        cri
Jami'in yankin Tonj a jihar Warrap dake arewacin kasar Sudan ta Kudu Makuei Mabior, ya bayyana a jiya Talata cewa, kwanan baya, a kalla mutane 118 sun rasa rayukansu a yankin sakamakon wata arangama da ta kaure tsakanin sojojin gwamnati da wasu mutane masu dauke da makamai.

Jami'in ya kara da cewa, a ranar 9 ga wata, sojojin gwamnati sun kama wani matashin dake dauke da makamai ba bisa doka ba, a lokacin da suke gudanar da aikin kwace damarar makaman dake hannun fararen hula ba bisa doka ba a wannan jiha. Gardamar da ta barke tsakanin sojoji da wannan matashi ta haddasa musayar wuta tsakanin sojojin gwamnati da mutane masu dauke da makamai, lamarin da ya haddasa rasuwar sojoji guda 34, da fararen hula guda 84, yayin da wasu suka jikkata.

Sai dai kuma, adadin wadanda suka mutu, na iya karuwa saboda rashin ingantaccen tsarin jinya a wurin.

Rahotanni na nuna cewa, a kasar Sudan ta Kudu, akwai mutane da dama dake rike da makamai, domin kare kansu saboda rikice-rikicen dake faruwa tsakanin kabilu daban daban. Wannan ya sa, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta yanke shawarar kwace makamai dake hannun fararen hula, amma, akwai mutane masu dake da makamai da dama da suka ki amincewa wannan shawara. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China