Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya bukaci a kai tallafin jin kai da tattalin arziki ga Sudan ta Kudu
2020-03-05 10:55:03        cri

Wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci kasa da kasa su ci gaba da samar da tallafin jin kan bil adama da na tattalin arziki ga al'ummar kasar Sudan ta Kudu, wadanda a kwanan baya suka kafa gwamnatin hadin kan kasa bayan shafe shekaru ana yakin basasa a kasar.

Da yake jawabi a taron kwamitin sulhun MDD game da batun kasar ta shiyyar Afrika, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana cewa, ya kamata duniya ta taimakawa kasar Sudan ta Kudu wajen warware matsalolin da suka addabe ta, kana a taimakawa kasar wajen sake maido da mutanen da tashin hankali ya raba da muhallansu.

Ya ba da shawarar a fadada zuba jari a kasar a fannonin aikin gona, makamashi, kayayayyakin more rayuwa, ilmi da fannin kiwon lafiya, domin taimakawa mutanen kasar Sudan ta Kudu don su samu damar farfadowa da sake gina gidajensu da samun bunkasuwa.

Mista Wu ya kuma yabawa kasar Sin bisa gudunmowar da ta baiwa tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu wajen aikin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kana ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bayar da taimako wajen aiwatar da yarjejeniyar farfadowar kasar ta shekarar 2018, tare kuma da wanzar da zaman lafiya a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China