Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Sudan ta Kudu zai sake nada Machar a matsayin mataimakin sa
2020-02-21 13:21:52        cri
A jiya Alhamis ne shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya sha alwashin sake nada Riek Machar a matsayin mataimakin sa na farko.

Salva Kiir ya ce a ranar Jumma'ar nan zai sanar da nadin Mr. Machar, wanda ke jagorantar rundunar 'yan tawajen SPLM-IO, kamar yadda hakan ke kunshe cikin yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da sassan biyu suka amince a shekarar 2018.

Shugaba Kiir ya ce tuni Mr. Machar ya amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa, tare da ci gaba da aiwatar da matakan warware batutuwan da sassan biyu ke takaddama a kan su.

Shugaban ya kuma jaddada cewa, matakan tabbatar da tsaro a birnin Juba, fadar mulkin kasar, za su ci gaba da kasancewa karkashin ikon sa, zai kuma samar da kariya ga daukacin jagororin 'yan adawa ciki hadda Mr. Machar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China