Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nada Guang Cong dan kasar Sin jami'in musamman a Sudan ta Kudu
2020-03-25 09:45:45        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Talata ya nada Guang Cong dan asalin kasar Sin a matsayin sabon mataimakin wakilin musamman na MDD mai kula da al'amurran siyasa a kasar Sudan ta Kudu kana mataimakin shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu (UNMISS).

Mr. Cong ya maye gurbin Moustapha Soumare dan kasar Mali, sakatare janar na MDDr ya yaba masa bisa rawar da ya taka wajen tafiyar da ayyukan MDDr a Sudan ta Kudu, kakakin babban sakataren ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka baiwa manema labarai.

Shi dai Mista Cong yana da kwarewar aiki wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa, kafin ba shi wannan matsayi ya rike mukamai daban daban a fannonin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China