Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mika kayayyakin yaki da cutar COVID-19 karo na biyu ga Nijer
2020-06-12 10:28:25        cri
A ranar 10 ga watan nan ne aka isar da kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 karo na biyu da gwamnatin kasar Sin ta samar ga janhuriyar Nijer a birnin Yamai, fadar mulkin kasar. A wannan rana kuma, ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijer din, ya mika wadannan kayayyaki ga ma'aikatar kiwon lafiya da ma'aikatar harkokin jin kai da daidaita matsala bayan aukuwar bala'u ta kasar.

Ministan harkokin jin kai da daidaita matsala bayan aukuwar bala'u ta jamhuriyar Nijer Magagi Laouan ya bayyana cewa, kasar Sin ta baiwa Nijer taimako matuka a fannin kiwon lafiya da sauransu. Kuma kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa Nijer din na wannan karo, za su ba da tabbaci ga Nijer, wajen cimma nasarar yaki da annobar, lamarin da ya nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

Kana, wakilin hukumar kiwon lafiyar duniya(WHO) dake Nijer, ya yi godiya ga kasar Sin, dangane da taimakon da take baiwa janhuriyar Nijer, da ma sauran kasashen duniya wajen yaki da annobar. Ya ce, kasar Sin ta zama abin koyi ga sauran kasashen duniya, kuma hukumar WHO za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin, da sauran abokanta na kasa da kasa, domin ba da taimako ga kasar Nijer, ta yadda za ta cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China