Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: kasar Sin za ta taimaka wajen gina wata duniya mai zaman lafiya
2020-08-10 21:47:38        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi bayani a yau Litinin, dangane da wasu abubuwan da kasar Sin za ta mai da hankali a kai, a fannin hulda da sauran kasashe.

Jami'in ya ce, kasar za ta yi kokari tare da sauran sassa don habaka hanyoyin musaya, da kara daidaita ra'ayi kan wasu manyan tsare-tsare, da hadin gwiwa da juna, don tinkarar koma bayan tattalin arziki, ta yadda za a gina wata duniya mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, wadda take rungumar ra'ayi na bude kofa, da cudanyar bangarori daban daban masu fada a ji, inda za a yi kokarin hadin gwiwa da juna don amfanar kowa, da ganin bayan cutar COVID-19, tare da gina wata al'ummar bai daya mai kyakkyawar makoma ta bil Adama. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China