Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kokarin taimakawa kamfanoni wajen rage harajin da suke biya
2020-08-09 16:51:47        cri
Ministan kudin kasar Sin Liu Kun, ya fada a jiya Asabar cewa, domin taimakawa kamfanonin da annobar COVID-19 ta haifar musu da mummunan tasiri, gwamnatin kasar tana kokarin rage musu harajin da suke biya. Tsakanin watan Janairu da na Yuni na bana, an rage haraji da sauran kudin da ya kamata kamfanoni su biya da yawansu ya kai kudin RMB Yuan biliyan 1504.5, ta yadda aka samu rage wa kamfanonin kasar wahalhalu sosai.
Mista Liu ya fadi haka ne, yayin da yake gabatar da wani rahoto ga zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin.
Duk a cikin wannan rahoto, an ce kudin da gwamnatin kasar Sin ta samu tsakanin watan Janairu da na watan Yunin bana, wanda za a maida shi cikin asusun kasafin kudin kasar, ya zarce Yuan biliyan 9617, adadin da ya ragu da kashi 10.8% bisa na makamancin lokacin bara. Sai dai tun daga watan Afrilu, an fara ganin wani yanayi na farfadowa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China