Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cui Tiankai: Muna cikin muhimmin lokacin daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka
2020-08-10 13:35:48        cri
Kwanan baya, jakadan kasar Sin dake kasar Amurka Cui Tiankai ya bayyana a birnin Washington na kasar Amurka cewa, yanzu, ana cikin muhimmin lokaci na daidaita dangantakar dake tsakanin kasar Sin da ta Amurka. Ya ce, zabin da aka yi a yau, zai tabbatar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yayin da zai ba da tasiri kan makomar kasa da kasa.

A ranar 4 ga wata, Cui Tiankai ya halarci taron dandalin tattauna batun tsaro na Aspen na shekarar 2020, inda ya yi shawarwari da shugaban tawagar manyan tsare-tsare na kungiyar Aspen game da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, sa'an nan, ya amsa wasu tambayoyin masu kallo.

A yayin da yake tsokaci kan tarihin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Cui Tiankai ya ce, daidaituwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da bunkasuwar dangantaka a tsakaninsu cikin shekaru da dama da suka gabata, ya dace da bukatun kasashen biyu, da na kasa da kasa. Akwai bambanci sosai a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a fannonin tarihi, al'adu, tattalin arziki da tsarin siyasa da sauransu, kuma wadannan bambance-bambance zasu ci gaba da kasancewa a tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci mai zuwa, amma bai kamata ya zama abinda zai hana ruwa guda wajen karfafa dangantakar dake tsakaninsu ba, a hakika dai, su ne damammaki ga kasashen biyu wajen karfafa hadin gwiwarsu da yin koyi da juna.

Ya ce, kasar Sin da kasar Amurka suna da bambanci, amma, ya kamata su hada kansu, domin fuskantar kalubalolin bai daya da kasa da kasa ke fuskanta, babu wata kasar da zata iya fuskantar wadannan kalubaloli a kashin kanta kadai. Shi ya sa, dole ne a yi hadin gwiwa da juna, a maimakon nuna kiyayya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China