Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Facebook ya cire wani hoton bidiyo da Donald Trump ya wallafa yana mai ikirarin garkuwar jikin yara na da karfi kan COVID-19
2020-08-07 15:38:03        cri
Facebook ya cire wani sako da Donald Trump, shugaban Amurka ya wallafa a ranar Laraba, ya na mai ikirarin garkuwar jikin yara na da karfi kan cutar COVID-19.

Sakon wani bidiyo ne na zantarwasa da kafar FoxNews da safiyar ranar Laraba.

A cewar kakakin kamfanin Facebook Andy Stone, bidiyon na kunshe da bayanai marasa sahihanci dake ikirarin cewa, garkuwar jikin wani rukunin mutane na da karfi kan COVID-19, wanda ya keta manufofinsu kamfanin na yaki da yada bayanan bogi game da COVID-19.

Ya kara da cewa, ainihin jawabin da ya keta ka'idojin Facebook shi ne ikirarin Trump na cewa kusan garkuwar jikin yara na da karfi kan COVID-19.

Ofishin yakin neman zaben Trump ya kuma wallafa wannan bidiyo a kafar Twitter, wanda ya dauko daga ainihin shafin shugaban kasar.

Kakakin ofishin, Courtney Parella, ta ce gaskiya shugaban yake fadi cewa, yara ba su da saukin kamuwa da cutar.

Ta kuma zargi Silicon Valley da nuna bangaranci, tana mai cewa, kamfanonin kafafen sada zumunta ba sa son tsage gaskiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China