Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya bada umarnin haramta amfani da TikTok nan da kwanaki 45
2020-08-07 14:15:32        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump a ranar Alhamis ya gabatar da dokar ofishin shugaban kasa inda Amurkar ta haramta yin duk wata hulda da kamfanin fasahar kasar Sin ByteDance, wanda ya mallaki shahararriyar manhajar nan ta bidiyo TikTok, dokar zata fara aiki nan da kwanaki 45, sai dai wannan mataki mai sarkakiya yana shan suka daga masana.

Sama da mutane miliyan 175 ne suka sauke wannan manhaja a Amurka, kana akwai mutane sama da biliyan daya da suka sauke manhajar a fadin duniya, kamar yadda dokar fadar shugaban kasar ta bayyana, wanda tayi ikirarin cewa, manhajar ta tattara wasu bayanai masu tarin yawa daga masu hulda da ita, inda suke wallafa sakonni masu barazana ga tsaron kasar Amurka.

Makamanciyar wannnan dokar an kuma bayar da ita ga manhajar aika sakonni da sada zumunta ta WeChat, wanda mallakin babban kamfanin fasahar kasar Sin ne Tencent.

A jawabin da ya gabatar a fadar White a farkon wannan mako, Trump ya fadawa 'yan jaridu cewa, kofarsa a bude take wajen kulla yarjejeniya da kamfanin fasaha na Microsoft ko kuma wani kamfanin kasar Amurka da ya sayi manhajar TikTok, inda ya bayar da wa'adin 15 ga watan Satumbar wannan shekara. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China