Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai yuwuwar dage fara harkokin cinikayya karkashin yarjajeniya ciniki cikin 'yanci ta Afrika
2020-05-30 16:30:42        cri
Akwai yiwuwar annobar COVID-19 da ake fama da ita yanzu, ta sanya a dage fara harkokin cinikayya a karkashin yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta Afrika, wanda a baya aka tsara zai fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli.

Prudence Sebahizi, shugaban sashen cimma yarjejeniya, kuma babban mai bada shawara ga yarjejeniyar cinikin cikin 'yanci, ya bayyana yayin wani taro ta kafar bidiyo a jiya cewa, an tsara shugabannin kasashen Afrika za su gudanar da taro a yau Asabar, 30 ga watan Mayu, domin amincewa da dukkan abubuwan da ake bukata na fara cinikayya a nahiyar a matsayin mara shinge.

Ya ce a yanzu, ba su san ko za a gudanar da taron ba, yana mai cewa, wannan zai iya tasiri kan fara harkokin cinikayyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China