Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta taimakawa mutanen da annoba ta shafa
2020-07-30 10:08:39        cri

Domin rage tasirin annobar COVID-19 ga mutane, hukumomin gwamnatin tsakiyar kasar Sin sun dauki matakai daban daban a watannin baya domin taimakawa mutanen da annobar ta shafa, kamar yadda ma'aikatar kula da jin dadin al'umma ta kasar Sin ta bayyana.

A cewar Jiang Wei, wani jami'in ma'aikatar jin dadjin al'umma ya fadawa taron manema labarai cewa, matakan da aka dauka sun hada da bayar da kudaden alawus-alawus, da bayar da kudaden rage radadi, da inganta hanyoyi da matakan neman tallafi.

Ya ce, wasu mutane da iyalai suna matukar bukatar agaji, sun hada da mutanen da suka rasa ayyukansu ko harkokin kasuwancinsu sakamakon annobar.

Jiang ya ce, gwamnatin tsakiya ta ware yuan biliyan 10.5 daga cikin sabon kasafin kudin da aka amince da shi wanda za'a taimakawa mutane masu fama da talauci wadanda annobar ta shafa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China