Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asibitin Huoshenshan ya fara karbar mutanen da suka kamu da cutar numfashi
2020-02-03 13:44:17        cri

 

Yau Litinin, an fara amfani da asibitin Huoshenshan mai gadaje 1000 a birnin Wuhan bayan an kwashe kwanaki 10 ana gina shi. Rundunar sojojin kasar Sin ta tura masu aikin jiyya 1400 a asibitin don kula da aikin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar.

Ran 23 ga watan Janairu, hukumar dake jagorancin aikin yaki da cutar numfashi a birnin Wuhan ta sanar da gina sabbin asibitoci a Caidian da Jiangxia, masu gadaje 1000 da 1500. Kwanakin baya-baya nan, aikin gina wadannan asibotoci sun jawo hankalin kasa da kasa, inda suke mamakin yadda Sin ta gina wadannan asibitoci biyu cikin kwanaki 10 kacal.

Ma'aikata fiye da 7000 daga wurare daban-daban na kasar Sin sun taru a Wuhan inda suke aiki ba dare ba rana don gina wadannan asibitoci. Bayan an kammala asibitin Huoshenshan, ma'aikata da kayan aiki suna ci gaba da aikin gina asibitin Leishenshan wanda zai kuma karbi mutanen da suka kamu da cutar. An ce, ya zuwa ran 2 ga wata, an kammala kashi 65 cikin 100 na aikin asibitin Leishenshan, inda aka kara gadajen zuwa 1600, ana saran kammala shi a ran 5 ga wata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China