Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin Mike Pompeo Na Kulla Kawancen Adawa Da Kasar Sin, Ya Danawa Kawayensa Tarko Ne
2020-07-23 20:34:48        cri

Ranar 22 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya kammala ziyarar da ya kai kasashen Birtaniya da Denmark. Abin da ya yi a lokacin ziyararsa bai wuce zaton mutane ba. A duk wuraren da ya ziyarta, abin da ya sha ambato shi ne batun adawa da kasar Sin, tare da yin kira a kafa wani sabon kawance don rage barazanar kasar Sin. Ya mayar da ziyarar da ya kai a Turai tamkar ziyarar neman samun kawayen adawa da kasar Sin. Amma sanin kowa ne cewa, yunkurinsa na rusa alaka a tsakanin Sin da kasashen Turai ba zai ci nasara ba, kuma hakan tarko ne kawai ya danawa kawayen Amurka.

Hakika dai, a shekarun da suka wuce, kasashen Amurka da Turai sun fuskanci sabani a fannonin kudaden tsaron da aka kashe, batun nukiliyar Iran, tattaunawar tattalin arziki da ciniki da kuma matsayin kungiyon kasa da kasa. Kuma a kwana a tashi huldar da ke tsakaninsu tana kara yin tsami.

Bana, shekaru 45 ke nan da kasar Sin ta kulla huldar jakadanci a tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai wato EU. Kamar yadda shugaban kasar Sin ya jaddada cewa, babu rikici a tsakanin Sin da Turai. Sun fi yin hadin gwiwa, a maimakon yin takara da juna. Kana suna da ra'ayi daya a wasu fannoni, a maimakon samun sabani. Bangaren Turai na da irin wannan ra'ayi. Madam Angela Dorothea Merkel, shugabar gwamnatin kasar Jamus, wadda ta fara shugabantar EUa wannan wata ta sake nanata cewa, hada kai da kasar Sin na da matukar muhimmanci ga EU ta fuskar manyan tsare-tsare. Yayin da huldar da ke tsakanin Amurka da Turai take kara yin tsami, kasashen Turai ba za su sadaukar da muradunsu ba, ba za su kuma fada tarkon da Amurka ta dana musu ba. Maganganun Mike Pompeo wadanda suka kawo wa Amurka da Turai illa duka, surutun banza ne kawai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China