Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana da kwararru sama da 150 na Amurka sun rubuta wasika a bayyane don zargin aikin dakile annoba na gwamnati
2020-07-26 17:27:02        cri
Kwanan baya, masana da kwararru sama da 150 sun rubuta wata wasika a bayyane, don yin kira ga shugabannin kasar da su tantance abubuwan da suka fi muhimmanci, su dakatar da sake farfado da tattalin arziki ba tare da bata lokaci ba, da kuma gayawa jama'ar kasar ainihin halin da kasar ke ciki game da dakile cutar COVID-19, har zuwa lokacin da ake iya shawo kan annobar kuma ake iya bincike kan wadanda suka yi mu'amala da masu kamuwa da cutar, za a yi gwajin farfado da tattalin arziki sannu a hankali.

Wannan wasikar da aka rubutawa shugaban kasar Donald Trump, da shugabanni na gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi daban daban na kasar, ta ce, kasar Amurka ta kasance kasar da aka fi samun yawan masu kamuwa da cutar a daukacin duniya, amma bisa wannan halin da ake ciki, kasar Amurka tana kokarin farfado da tattalin arziki, hakan ya sa mutane masu yawa sun gamu da bala'in cutar, ta yadda yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar da wadanda suka mutu sakamakon cutar yake karuwa cikin sauri.

Wasikar ta yi kira ga shugabannin da su saurari ra'ayin kwararru, ta kuma nuna cewa, "abu mafi muhimmanci ga Amurka a halin yanzu ba farfado da tattalin arziki ba ne, a maimakon haka ya kamata a ceto rayuwar mafi yawan al'ummar kasar".

Bisa kididdigar da cibiyar shawo kai da rigakafi kan cutuka ta kasar Amurka ta bayar a ranar 24 ga wata, an nuna cewa, a karo na hudu ne yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a cikin rana daya ya wuce dubu 70, wato ya kai 72,219, ke nan yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya riga ya wuce miliyan 4, wanda ya kai 4,024,492. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China