Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana: Muguwar halayyar da Amurka ke nunawa Sin barazana ce ga zaman lafiyar duniya
2020-07-26 17:20:18        cri
Masanan kasa da kasa sun bayyana a ranar Asabar cewa, kalaman rashin dattakun da gwamnatin Amurka ke furtawa da muguwar halayyarta kan kasar Sin yana kara haifar da barazana ga zaman lafiyar duniya, kuma lamarin zai iya zamewa sabon yakin cacar baka kan kasar Sin wanda hakan ya saba da hakkokin bil adama.

Tsokacin ya zo ne a lokacin taron tattaunawa ta kafar bidiyo mai taken yunkurin kasa da kasa na nuna adawa da sabon yakin cacar baka kan kasar Sin, wanda ya samu halartar kwararru daga kasashen duniya masu yawa da suka hada da Amurka, Sin, Birtaniya, Indiya, Rasha da Kanada.

Jenny Clegg, kwararriyar malama a sashen nazarin al'amurran kasa da kasa ta jami'ar Central Lancashire, tace, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana daya daga cikin muhimman dangantaka a tsakanin kasashe kuma lalacewarta zai iya zama babbar barazana ga zaman lafiyar duniya.

Medea Benjamin, wacce ta kafa kungiyar Codepink, wata kungiya ce da mata ke jagoranta da nufin kawo karshen yake-yake a Amurka, tace, ta nuna damuwa kasancewa shugabannin Amurka sun yi ikirarin cewa kasar Sin tana aiwatar da sabbin hanyoyi na tsokana a yayin da Amurka ce ita da kanta ta kafa sansanonin sojoji a sassan duniya.

Magaret Kimberley, wata marubuciyar kafar Black Agenda Report, tace, gwamnatin Amurka tana yin mummunan kage kan kasar Sin game da batutuwan dake shafar jahar Xinjiang, da batun yaki da annobar COVID-19, da kuma tilasta rufe karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston matakin da ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Wasu kwararrun dake halartar taron sun fitar da sanarwa, inda suka bukaci bangaren Amurka da ta kaucewa wannan barazanar yakin cacar bakan, kana ta nisanci aikata duk wasu abubuwa da ka iya zama mummunar barazana ga zaman lafiyar duniya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China