Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Nuna goyon baya ga juna da hada kai tare su ne hanyoyi na tinkarar matsaloli
2020-07-28 20:36:23        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da jawabi a yayin taron shekara-shekara ta kafar bidiyo, na majalisar bankin AIIB da aka shirya a yau Talata, inda ya nuna cewa, yadda daukacin duniya ke dakile yaduwar annobar numfashi ta COVID-19 ya nuna cewa, dan Adam yana da makoma ne ta bai daya. Kuma ko shakka babu, ta hanyar nuna goyon baya ga juna, da hada kai tare ne kawai za a iya warware matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce, a yayin da ake kokarin warware matsalolin da suka bullo, a yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya, ya kamata kasashe daban daban su kara yin hakuri da juna wajen gudanar da harkokin duniya, kuma su kare tsarin cudanyar bangarori da dama mai amfani, da kuma yin hadin kai mafi yakini a yankin.

A cewarsa, kamata ya yi bankin AIIB ya kasance wani sabon dandamali na kasashe mambobinsa, wanda zai inganta samun bunkasuwa tare, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China