Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ko da yaushe kasar Sin na tsayawa kan ra'ayin cudanyar bangarori da dama
2020-07-28 20:28:53        cri
A yau Talata ne aka bude taron shekara-shekara ta kafar bidiyo, na majalisar bankin AIIB karo na 5. A yayin da yake jawabi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ko da yaushe kasarsa, na tsayawa kan goyon baya, da aiwatar da ra'ayin cudanyar bangarori da dama, da kuma bin tunanin bude kofa ga kasashen waje, da hada kai da samun nasara tare, wajen neman ci gaba tare da kasashe daban daban.

Shugaba Xi ya ce kasarsa za ta ma ci gaba da kokari tare da kasashe mambobin AIIB, don nuna goyon baya da gudanar ga ayyukan bankin yadda ya kamata, kana za ta kara taka rawa a fannin tinkarar kalubalolin da kasashen duniya ke fuskanta, da tabbatar da samun bunkasuwa tare. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China