Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya yi kira da a mayar da AIIB sabon dandalin gina al'umma mai makomar bai daya ga bil Adama
2020-07-28 19:18:40        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a mayar da bankin zuba jarin samar da ababen more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice, matsayin sabon dandalin gina al'umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama.

Shugaba Xi ya yi wannan kira ne a Talatar nan, yayin da yake jawabin bude taron shekara shekara karo na 5 na bankin ta kafar bidiyo. Ya ce yana fatan ganin bankin na AIIB ya zama dandalin da zai bunkasa ci gaban daukacin kasashe mambobin sa, da ma sauran sassan duniya baki daya.

Kaza lika ya yi fatan kasancewar bankin wani sabon dandali da ke tafiya tare da zamani, wanda kuma zai haifar da hadin gwiwar kasa da kasa.

An dai kaddamar da ayyukan bankin na AIIB ne a shekarar 2016, bayan da shugaba Xi ya gabatar da shawarar kafuwarsa a shekarar 2013.

A lokacin kafuwar sa, bankin na da mambobi ne 57, amma ya zuwa yanzu yawan mambobin sa sun kai 102, daga nahiyoyi 6 ciki hadda kasashen Asiya, da Turai, da Afirka, da Arewacin Amurka, da kudancin Amurka da kuma Oceania. Bankin ya kuma kara karfi matuka tun kafuwarsa kawo yanzu, inda ya samar da jarin gina ababen more rayuwa ga mambobin sa, wadanda suka kai kusan dalar Amurka biliyan 20.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China