
Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayar a shafin yanar gizo, a jiya 27 ga wata, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 68, daga cikinsu, guda 4 sun shigo ne daga kasashen ketare, kana 64 sun fito ne a cikin kasar Sin, wadanda suka hada da mutane 57 daga yankin Xinjiang, da mutane 6 daga lardin Liaoning, sai kuma mutum daya daga birnin Beijing. Hukumar ta kara da cewa, babu wanda ya mutu sakamakon cutar, kana babu wanda ake shakkun ko ya kamu da ita ko a'a.
Yawan mutanen da suka warke daga cutar COVID-19 a wannan rana ya kai 16, sannan mutane 184 sun fita daga matakin killacewa. (Zainab)