Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompeo wanda yake yunkurin tada yakin cacar baki zai kawo illa ga zaman lafiyar duniya
2020-07-27 15:44:37        cri
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi jawabi a laburaren Nixon dake jihar California, inda ya ba da ra'ayin barazanar kasar Sin, ya ce, a cikin shekaru 50 da suka gabata, manufofin Amurka kan kasar Sin ba su yi nasara ba, inda ya yi kira ga kasar Amurka da kasashe kawayenta da su dauki karin tsauraran matakai don canja kasar Sin. Wannan jami'in da bai san ya kamata ba, dake gudanar da harkokin wajen kasar Amurka yana yunkurin tada yakin cacar baki, wanda zai kawo babbar illa ga zaman lafiyar duniya.

A cikin jawabin Pompeo, ya nuna shakka ga duk wani hadin gwiwa da mu'amala dake tsakanin Sin da Amurka, a ganinsa Sin ta cimma moriya.

Amma mene ne gaskiyar batun? Babu shakka ba haka ba ne. Game da zuba jari ga kasar Sin, kamfanonin kasashen waje ciki har da na kasar Amurka sun zuba jari da kafa kamfanoninsu a kasar Sin, wadanda suka samu sauki. Kana an iya sassauta hauhawar farashin kaya na duniya ta hanyar samar da kayayyaki kirar Sin masu araha da inganci, ta hakan masu kashe kudi da masu zuba jari dukkansu za su samu moriya. Wannan ya shaida cewa, Sin ba ta kawo barazana ga tsarin zaman rayuwar mutanen Amurka ba, sai dai tabbatar da shi.

Bisa tarihin shiga duniya da kasar Sin ta yi a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, Sin tana son kiyaye zaman lafiya, kuma ba ta kama karya a duniya. Har ila yau, Sin ta kawowa duniya dama, ba barazana ba, kuma Sin tana son zama abokiya, ba abokiyar gaba ba. A cikin duniyar dake da bangarori daban daban, Sin da sauran kasashen duniya suna da dangantakar juna, ba abu ne mai yiwuwa ta koma yanayin yakin cacar baki ba.

Pompeo ya ba da ra'ayin da bai samu amincewa daga dukkan duniya ba, tare da yunkurin tada rikici don sa kaimi ga raba Sin da sauran duniya, wanda bai dace da moriyar jama'ar kasa da kasa na duniya ba, kuma kasa da kasa sun yi Allah wadai da ra'ayin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China